Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Babban Malamin Addinin Musulunci A Nigeria

Tarihin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Babban Malamin Addinin Musulunci A Nigeria


Malamin ya kware musamman a bangaren Al-Qur’ani na Tafsirinsa da kuma sanin ilmin sa da kira’o’in sa da kuma dalilan saukar ayoyin ciki. Malamin ya karantar da al’umma a Kano, Maiduguri, Kaduna, Katsina da kuma Bauchi. 


Kamar yadda Malamin ya fada daga cikin malamansa na ilimin addinin Musulunci, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago da ke cikin Kano. A wajen Malam Dandago ne Marigayin ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi. Sauran Malaman sun hada da Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu da sarfu da balaga da adab. Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Har yanzu wannan babban Malami na Hadisi Ahmad Ibrahim.


Daga cikin malamansa na jami'a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi'u da Dr. Khalid Assabt da sauran su.


Karatu da darusan da Malam ya koyar a rayuwarsa Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma. Ja’afar Adam ya sauke Al-Qur’ani kusan sau 2 a Masallacin Muhammad Indimi da ke cikin Garin Maiduguri a jihar Borno, a cikin shekaru barkatai. Malam ya kuma karantar da Kitabuttauhiid na Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahab, da kuma littatafan hadisai na Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith. Sauran darusa sun hada da wani littafin tauhidi da ya fice mai suna Kashfusshubuhaat.


Haka kuma Malam ya karantar da litaffin nan na Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, da kuma Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy na Muhammad Nasirud Deen Albany. 


Almajirai 


Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi'u Umar R/Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Malam Abdullah Usman Gadon Kaya da Malam Usman Sani Haruna da kuma Malam Ibrahim Abdullahi Sani. Sauran manyan Almajiran Marigayin sun hada da Malam Ali Yunus Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da kuma Malam Anas Muhammad Madabo. 


Kafin rasuwarsa, Malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre). 


Ja'afar Mahmud Adam malamin addinin Islama ne Ra'ayin Salafawa dan Najeriya kuma dan kungiyar Jama'atu Izalat al Bid'a Wa Iqamat as Sunna, kungiya ce mai zaman kanta a Kano tare da Maiduguri a matsayin wurin gudanar da tafsirin watan Ramadan


An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a  A Ranar 12 Ga  Watan Fabrairu shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara

karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam

Haruna, wanda kuma dan'uwansu ne na jini.


Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakaninsu, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. 


Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano. Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. 


Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adul Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru

na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne

mafi kankanta a ajinsu. 


Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988.


A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take Khartoum, Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya gama.


Rasuwarsa😡.


Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (daidai da 13/04/2007). Malamin ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan an yi masa kisan gilla. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi. 


Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan Aljannatul-firdaus

Post a Comment

Previous Post Next Post