Mummunar Ambaliyar Ruwa Na Barazana A Wasu Sassan Jihar Kano - Rahoto Jabiru Hassan

Mummunar Ambaliyar Ruwa Na Barazana A Wasu Sassan Jihar Kano - Rahoto Jabiru Hassan


A DUK lokacin da aka sami faduwar damina, ambaliyar ruwa tana haifar da cunkoson ababen hawa da lalacewar hanyoyi da rugujewar gidaje da gonaki harma wasu lokutan ana samun asarar rayuka wanda ya kan haifar da matsala ga al’umma don haka lokaci ya yi da gwamnatoci zasu kara himma wajen daukar matakai na magance wannan matsala.

Wakilin mu ya gudanar da zagaye domin duba yadda ambaliyar ruwa ke haifar da matsaloli a wasu sassan na birnin Kano da kewaye, ya ruwaito cewa idan damina ta sauka, ana yawan samun matsalar ambaliyar ruwa musamman a cikin wasu unguwanni da rukunin gidaje na gargajiya da Kuma gefen tituna.

Cikin dalilai da suke jawo ambaliyar ruwa akwai toshewar hanyoyin ruwa kamar magudanun ruwa da ajiye kasa ko yashi ko Kuma dutsen gini daidai hanyar ruwa da kumu yin gine-gine kan hanyoyin ruwa wanda hakan ke jawo ambaliyar ruwa da rugujewar muhalli.

Sannan akwai rashin bin ka’idojin yin gine-gine daga al’umma, inda sau tari mutane suna yin gini ba tare da an duba tsarin ginin ba wanda hukumomin kula da muhalli ke bayarwa da kuma tara shara daidai hanyar ruwa watakila saboda rashin wadatar guraren ajiye shara.

Da yake zantawa da wakilin mu, tsohon shugaban kwamitin koli na kungiyoyi aiyukan gayya na Jihar kano Kuma shahararren magini, Alhaji Ibrahim Garba Aminu Kofar Na’isa ya bayyana cewa akwai abubuwa masu yawa dake haddasa ambaliyar ruwa amma mafi girma cikin dalilan shi ne tare hanyoyin ruwa da Kuma rashin bin ka’idojin yin gine-gine.

Sannan ya bayyana cewa ta fannin yashe magudadun ruwa da bubbude hanyoyin ruwa wajibi ne a yabawa gwamnatin Jihar kano musamman yadda ake baiwa kungiyoyin taimakon kai da kai kwarin gwuiwar gudanar da aiyukan tsaftace muhalli da gyara magudanun ruwa kafin zuwan damina.

Ya ce “a matsayina na Dan kungiyoyin aiyukan taimakon kai da kai, na tabbatar da cewa Jihar kano tana Kan gaba wajen kula da muhalli da kuma kokarin magance yawaitar ambaliyar ruwa da ake samu a fadin Jihar, don haka ko shakka babu gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta cancanci yabo ta fuskar kula da muhalli.

Shi ma a nasa tsokacin, Alhaji Usman B. Dan Gwari, mazaunin Rijiyar Lemo yankin Karamar hukumar Fagge, ya bayyana cewa gwamnati tana bakin kokarin ta wajen kyautata muhalli, sai dai mafiya yawan lokuta mutane suna toshe hanyoyin ruwa domin samun damar yin gine-gine wanda hakan ba daidai bane.

Ya yi amfani da wannan dama wajen yin Kira na musamman ga hukumomin dake kula da muhalli da su taimaka wajen ganin an magance ambaliyar ruwa dake addabar masu ababen hawa tun daga layin yan Babura zuwa daidai kwanar jajira wanda da zarar anyi ruwa ana samun cunkoson ababen hawa saboda yadda ruwa ke zama kan titin.

Sannan ya bukaci al’umma da su daina toshe hanyoyin ruwa domin samun guraren yin gine-gine inda kuma ya yaba wa yan kungiyoyin aikin gayya na Jihar Kano bisa yadda suke kokari sosai wajen ganin ana samun nasarar magance ambaliyar ruwa a birni da kewayen kano.

Wakilin mu ya ziyarci bakin sha tale-tale na Baban Gwari, hanyar Gwammaja, Gyadi-Gyadi, Titin gilin girgin sama da unguwar Sabon Gari da kuma Badawa inda Gaskiya Tafi Kwabo ta duba yadda masu ababen hawa harma da masu tafiya a kasa suke fama da ambaliyar ruwa kan tituna da lunguna.

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post