Yadda Wata Kotu Ta Amince A Kashe Mawakin Da Ya Yi Batanci Ga Annabi Muhammad (S.A.W) a Nigeria.
Wata Kotun Daukaka Kara ta Tarayya da ke jihar Kano a Najeriya, ta amince da hukuncin kisa da kotun shari’ar musulunci ta jihar ta yanke wa mawakin nan Yahya Aminu Sharif, wanda ya yi batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Kotun ta amince da hakan ne a wani zama na minti 17 da ta yi Ranar Laraba ta kafar bidiyo.
Alkalin da ya jagoranci zaman, Abubakar Mu’azu Lamido ya ce, an yi watsi da daukaka karar Yahya Aminu Sharif, saboda ba ta da armashi.
A cikin watan Agustan shekarar 2020 ne, Kotun Shari’ar Musuluncin ta yanke wa Sharif hukuncin kisa ta hanya rataya bisa wasu kalamai da ake kallo a matsayin sabo da ya furta kan Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallam.
Mawakin ya daukaka kara domin kalubalantar hukuncin, kuma a cikin watan Nuwamban 2020, kotun jihar Kano ta yi watsi da hukuncin kisan tare da bada umarnin sake gudanar da shari’ar a gaban Kotun Daukaka kara ta Shari’ar Musulunci.
Saidai lauyoyin da ke kare Sharif na masu neman a yi masa shari’a a kotun da babu ruwanta da addini.
Report: Hausa Tv
Tags
Rahoto