An Samu Nasarar Tarwatsa Shirin 'Yan Fashin Daji na Haɗa Bom da Buhu 27 na Takin Zamani A Jihar Kaduna

An Samu Nasarar Tarwatsa Shirin 'Yan Fashin Daji na Haɗa Bom da Buhu 27 na Takin Zamani A Jihar Kaduna


Rundunar Jami'an tsaron Najeriya sun kama buhun takin zamani 27 da ake zargin 'yan fashin daji na shirin haɗa abubuwan fashewa da su a Jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.


Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna Samuel Aruwan ya fitar ta ce dakaru sun far wa sansanin jagoran 'yan fashi Lawal Kwalba bayan sun samu bayanan sirri a yankin Dende na Ƙaramar Hukumar Chikun.

 

Jami'an sun gano batiri-batiri da kuma buhuhunan takin zamani 27...waɗanda ake kyautata zaton za su haɗa abubuwan fashewa da su ganin irin alaƙarsu da 'yan ta'adda (Boko Haram)," a cewar Mista Aruwan.


Hakazalika, jami'an tsaro sun gano babur ɗaya da wayar salula biyu a sansanin bayan 'yan bindigar sun tsere kafin dakarun su cim musu.


Sannan, An kama wasu mutane a yankin bayan jami'an tsaron sun ci gaba da bin sawun su kuma ana ci gaba da bincike kan su, a cewarsa.


Report: Bbc Hausa

Post a Comment

Previous Post Next Post