BINCIKE: Akalla An Kashe Mutane 465, Sannan An Yi Garkuwa da 355 A Cikin Watan Yunin Da Ya Gabata A Nigeria.
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna “Connected Development (CODE) a tarayyar Najeriya ta fidda rahoto dangane da al-amuran tsaron kasar, inda ta bayyana cewa cikin watan Yunin da ya gabata an kashe mutane 465 tsakanin jami’an tsaro da fararen hula, sannan an yi garkuwa da wasu 355 a cikin watan.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban bangaren bincike na kungiyar Ani Nwachukwu yana cewa mutane akalla 2000 ne suka kauracewa gidajensu sanadiyyar matsalolin tsaro a cikin watan a duk fadin kasar.
Rahoton ya kara da cewa duk tare da cewa yawan kudaden da gwamnatocin tarayyar da na jihohi suke kashewa bangaren tsaro yana karuwa a ko wace shekara amma matsalolin tsaro sai karuwa suke yi.
Daga karshen kungiyar ta bayyana cewa akwai bukatar a bincike hukumomin tsaron kasar don sanin inda wadannan makudan kudaden ake kashewa bangaren tsaro suke tafiya, ba tare da an ga wani ci gaba a harkokin tsaron kasar ba.
Report: Hausa Tv
