IN HAR NACI ZABE: Matsalar Wutar Lantarki Za ta Zama Tarihi A Najeriya – Atiku Abubakar
Dan takarar shugabancin Nijeriya a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, kasar za ta samu wadatacciyar wutar lantarki.
Atiku Abubakar dai na magana ne game da yajin aikin da ma’aikatan kamfanonin samar da lantarki na kasar suka shiga da hakan ya yi sanadiyyar rasa wutar a duk fadin kasar.
Sai dai Atiku a shafinsa na Twitter da Daily Trust ta bibiya, ya wallafa cewa zai mayar da hankali sosai wajen ganin matsalar ta zama tarihi a Nijeriya.
DCL Hausa ta ba da labarin cewa bayan tsunduma yajin aikin ma’aikatan lantarkin, sai kuma suka sanar da janye yajin aikin bayan wata yarjejeniya da suka ce idan ba a cika musu ba, za su sake komawa nan da makonni biyu.