Wallahi: Sai Inda Karfina Ya Kare Wajen Yaki Da Shan Kwaya A Nijeriya - Aisha Buhari

Wallahi: Sai Inda Karfina Ya Kare Wajen Yaki Da Shan Kwaya A Nijeriya - Aisha Buhari


Uwargidan shugaban Nijeriya Hajiya Aisha Buhari ta ce sai inda karfinta ya kare wajen yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin matasa maza da mata a kasar.

A taron fadakarwa kan yaki da shan kwaya na shekarar 2022, Aisha Buhari ta bukaci masu ruwa da tsaki da su hada hannu waje guda domin ganin an yi wa tufkar hanci a duk fadin kasar.

A cikin wata sanarwa daga mai taimaka wa uwargidan shugaban kasar ta fuskar watsa labarai Sani Zoro da DCL Hausa ta samu kwafi, ta bukaci masu sarautun gargajiya da su ci gaba da ba da irin gudunmuwar da suka saba wajen ganin matsalar ta kaura a tsakanin matasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post