Tabbas Yunwa Za ta Yiwa Wadannan Jihohin Najeriya 16 Katutu A Arewacin Najeriya - Majalisar Wakilai
Majalisar Wakilan Nijeriya ta ce ganin yadda matsalar tsaro ke kara rincabewa a kasar, ne ake ganin karancin abinci zai yi kamari a jihohi 16 na kasar.
Majalisar kamar yadda Daily Trust ta rawaito, matsalar na da alaka da yadda ‘yan ta’adda ke yi wa manoma kwanton-bauna tana kashe su, ta kori mutane daga kauyukansu tare da tilasta wa mutane su biya kudin fansa ga ‘yan’uwansu da aka sace.
Majalisar ta bukaci kwamitocin da ke da alaka da aikin gona da su hada hannu da hukumomin da ke da alhaki domin taro matsalar tun da wuri.
Hakan kamar yadda majiyar DCL Hausa ta jiyo, ya biyo bayan wani kudiri da dan majalisar Rimamnde Shawulu ya gabatar a zauren majalisar, inda ya ce ko a kwana-kwanan nan da bankin CBN ya fitar da sanarwa, ta nuna cewa Nijeriya ta kashe kudi Dala bilyan 2.7 domin shigo da abinci a shekarar 2021.